Rashin Asibiti na kashe mata masu ciki a garin Jagindi, Kudancin Kaduna

0

A kalla mata masu ciki biyar ne suke rasa rayukansu duk wata a masarautar Jagindi Tasha dake Godogodo a karamar hukumar Jema’a, jihar Kaduna.

Mai anguwan Jagindi Tasha Danlami Barde ne ya fadi hakan wa manema labarai a wata taro da hukumar wayar da kan mutane ta kasa wato National Orientation Agency NOA da UNICEF suka shirya a garin Kachia.

Basaraken ya yi bayanin cewa rashin kwararun ma’aikata a asibitin dake kauyen ya sa mata masu juna biyu kan rasa rayukansu wanda hakan ya kan sa dole su tafi asibitin Kafanchan wanda ke da nisan kilomita 35 domin samun kulan da suke bukata.

wasu mata har biyar sun rasa rayukansu a hanyarsu na zuwa Kafanchan a watan Janairun da ya gabata.

Bayan haka Barde ya yi kira ga gwamnati da ta taimaka ta gina musu asibiti kusa da su wanda matan su za dunga zuwa da zarar suna bukatar hakan ko kuma haihuwa ta ta zo.

Masarauta 150 ne daga yankin suka halarci taro.

Share.

game da Author