Shahararren mawakinnan Rarara ya saki wata sabuwar waka domin murnar dawowar Shugaban kasa Muhammadu Buhari kasa Najeriya.
Rarara ya kuranta sannan ya yabi Buhari kuma ya yi masa addu’ar samun karin lafiya.
Buhari ya dawo kasa Najeriya daga kasar Britaniya bayan dauke kwanaki 51 da yayi a can yana hutu sannan kuma ya na ganin likitocinsa.
Shugaban kasan ya sauka kasa Najeriya ne ranar Juma’a da safe inda ya wuce kai tsaye zuwa fadar Shugaban kasa dake Aso Rock.
A jawabin da yayi bayan ya shiga gida, ya godewa mataimakin Shugaban kasa sannan kuma ya jinjina wa ‘yan Najeriya kan addu’o’i da sukayi ta yi masa a lokacin da yake kasar Britaniya
Sauraren waka a nan: https://youtu.be/1VAw5235q-c