Ranar Ruwa ta Duniya: Matsalar rashin taftaccen ruwan sha

0

Ranar 22 ga watan Maris ta kowacce shekara rana ce da a kan yi bikin ranar ruwa ta duniya da nufin wayar da kan al’umma game da muhimmancin amfani da tsaftataccen ruwan sha.

A kowace shekara dai masu wannan bikin kan yi nazari kan wani maudu’i guda daya da ya shafi ruwa mai tsafta inda taken bikin na bana shi ne ”Dalilan da ke sa ake barnar ruwa”.

A shekarar 1993 ne aka fara bikin wannan rana, domin tunasar da al’ummar duniya muhimmancin samun tsaftataccen ruwa sha.

Majalisar dinkin duniya da wasu kungiyoyi masu zaman kansu kan yi amfani da wannan rana wajen shirya abubuwa da dama a kan yadda za a amfana da wannan rana.

Yawanci dai kasashen masu tasowa na fama da matsalar samun tsaftataccen ruwa, wanda hakan ke jefa dumbin jama’a cikin mawuyacin hali kamar kamuwa da cutuka da dai makamantansu.

A Najeriya ma dai ana fuskantar matsalar rashin ruwa mai tsafta, kuma rashin ruwa da muhalli mai tsaftar na haddasa mutuwar yaran da ba su kai shekara biyar ba a kasar.

Batun samar da ruwan matsala ce da jama’a da dama akasari daga yankunan karkara musamman a kasashe masu tasowa irin Najeriya suka dade suna fama da ita inda a wasu lokutan sukan bige da amfani da gurbataccen ruwa daga tafkuna.

A bangare guda kuwa, hukumar kula da yara ta Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ta yi gargadin cewa yara kimanin miliyan shida, a fadin duniya, ka iya tsintar kansu a muhallan da ke da tsananin kamfar ruwa, a shekara ta 2040.

Masana sun dai yi hasashen cewar batun cimma burin samar da ruwan sha mai inganci da wadatuwa a kasashen duniya wani babban kalubale ne ga hukumomin na suga cewar sun bi kammalallen tsarin bai daya na sarrrafa albarkatun ruwan.

Daga Ahmadu Manaja Bauchi.

Share.

game da Author