Najeriya bata bukatan ministocin Kiwon Lafiya da na Ayyukan Gona – Inji Atiku Abubakar

0

Tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya ce ya kamata a sake duba tsarin mulkin kasa Najeriya musamman yadda ya ba gwamnatin tarayya iko fiye da na jihohi.

Atiku ya ce hakan ya sa ana samun karancin ci gaba a musamman a jihohi, kananan hukumomi da gundumomi.

Ya kara da cewa ba daga Abuja bane ya kamata a ce wai ana nada ministoci irin na kiwon lafiya da na ayyukkan gona domin a ganinsa a jihohi ne ya kamata ayi hakan ba daga tsakiya ba.

Ya ce babu ruwan gwamnatin tarayya da nada ministoci a wannan ma’aikatu guda biyu, abinda ya kamata ayi shine a kirkiro wasu hukumomi ko ma’aikatu da zasu sa ido da kuma kula da ma’aikatun a jihohi.

Atiku yace irin tsarin mulkin da Najeriya ta ke yi da komai sai daga Abuja ba tsari bane da zai sa a samu ci gaba mai dorewa musamman a jihohi da kananan hukumomi wanda a can ne aka fi bukatan irin wadannan ayyuka.

Ana rade-radin cewa Atiku Abubakar na shirin sake fitowa takaran Shugaban cin Najeriya a 2019.

Share.

game da Author