A shekaran 2015 shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da shirin tallafawa wa manoma da bashi domin bunkasa noman shinkafa a jihar Kebbi.
Shirin mai suna Anchor Borrowers’ Programme (ABP) a turance zai taimaka wa manoman jihar da kudade da kayayyakin noma domin samun sauki da Karin yabanyar su a noman wannan shekara.
Wadanda suka amfana daga wannan shiri sun hada da manoman kananan hukumomin Argungu, Bagudo, Augie, Kangiwa, Kalgo da Yauri.
Shirin ABP na taimakawa manoma kudaden da za su bukata domin nomar shikafa na akalla gona mai fadin hekata daya da kuma kamfanonin da ke sarrafa shinkafan.
Da yake bada baynai akan amfana da yayi da shirin ABP, wani magidanci Umaru Salihu yace shirin ta taimaka masa wajen nasarorin da ya samu a nomar bana.
Yace shi ma’aikacin gwamnati ne kuma ya na karban albashin naira 34,000 a wata inda kafin watan ta kare ya kashe kudin amma da taimakon Umaru Alhassan, shugaban kungiyar manoman shinkafa na karamar hukumar Jega ya shiga cikin shirin inda ya fara da noma hekta daya na shikafa.
Salihu yace a yanzu haka hekata 10 gareshi wanda 5 ne kawai yake noman shinkafa akai kuma hakan yasa ya na iya ciyar da iyalansa iya gwargwado batare da wata matsala ta jiran albashi.
Shugaban kungiyar manoman shinkafa na karamar hukumar Jega Alhassan Umaru yace tun da gwamnatin Buhari ta bullo da wannan shiri a yankunan su matasan yankin musamman zauna gari banza da kuma ‘yan ci rani sun koma gona domin aiki ta samu a jihar Kebbi.
A wata hira da gidan jaridar PREMIUM TIMES ta yi da mataimakin gwamnan jihar Kebbi Samaila Yombe, kwamishanan noma Garba Dadinga da sakataren ma’aikatan noma ta jihar Muhammed Lawal sunce adadin yawan mutanen da suka amfana da shirin sun kai yawan 78,000 a jihar.
Wasu ma’aikatan gwamnati da wasu manoma sun ce sun karbi bashin kudaden da suke bukata domin noma hekta daya ne kawai amma a wata bayanai da ta fito daga babban bakin Najeriya (CBN) ta nuna cewa yawan gonakin noman ya fi manoman yawa wanda hakan ya nuna cewa wadansu na noma fiye da hekta daya kenan.
Manajan kungiyar Labana Rice da ke jihar, Abdullahi Zuru ya tabbatar da cewa babu manomin da ke noma fiye da hekta daya kamar yadda babban bankin kasa ta ce.
A dalilin haka manoman da muka ziyarta sun fadi irin abubuwan da suka amfana dasu da kuma yadda suka karbi nasu basukan da taimakon.
Wani manomi a garin Augie Aliyu Shehu yace gwamnati bata tabbatar da gonakin da ake nomawa ba ta dai basu kudaden ne kawai.
Wasu manoman da suka yi rajista da kungiyoyi masu zaman kansu, Malam Shehu manomin shikafan rani da ta damina, da wani Malamin jami’a wanda baya so a fadi sunansa, Hafiz Sanusi da Mallam Kashibu a kauyen Kwallaga dake garin Argungu sun ce su kam gwamnati ta zo ta duba gonakin da suke nomawa bayan sun samu taimakon.
Wani jami’In babban bankin Najeriya Isaac Okorafo ya ce bankin ta turo ma’aikatan koyar da dabarun noma wato (extension workers) domin su koyar da manoma sabbin dabarun noman tare da samar musu da inshawura daga kamfanin NAIC.
A binciken da gidan jaridar PREMIUM TIMES ta yi ba ta ga alamar aikin da kamfanin inshora na NAIC ta yi ba kuma manoman basu ce sun sami wata inshora ba sai dai manoman da basu yi amfani da kudaden da suka karba ban a tallafi a shekaran bara sun ajiye kudaden sa a damunan bana.
A yanzu hakan mataimakin gwamnan jihar Kebbi Yombe yace su na kokarin hada uwar kudin tare da ribar da manoman za su bayar domin maida wa babban bankin Najeriya.
A wata hiran da gidan jaridar PREMIUM TIMES ta yi da shugaban Labana Rice malam Zuru y ace shirin ABP ya kawar da matsalar rashin siyar da kayan gona da manoma ke fama da shi. Ya ce manoman za su iya siyar wa gwamnati su kuma su siyar wa kamfanonin da ke sarrafa shinkafa ko kuma su sayar wa ‘yan kasuwa.
Zuru ya kuma ce babban bankin kasa CBN ta amince manoman su yi amfani da kudaden da suka karba a damunan badi saboda matsalar da aka samu wajen biyansu kudaden da wuri har lokaci ya kure.