Malaman makarantar firamare biyu sun yi ma daliban su fyade a jihar Bauchi

1

A ranan alhamis ne 16 ga watan Maris 2017 rundunar ‘yan sandar Jihar Bauchi ta gurfanar da wasu malaman makarantan firamare da ke Unguwan Dutsen Tashi dake garin Bauchi a gaban kotu bisa zargin aikata laifin fyade ga wata daliban su.

Kwamishinan yan sandar Jihar Garba Baba Umar, yace wadanda ake zargin sun lallabi yarinyar ne zuwa wani wuri in da suka aikata fyaden a kanta.

Kamar yadda Ahmadu Bauchi ya sanar mana, Malaman makarantan dan Shekara talatin da tara ne 39 da kuma dan Shekara talatin da uku 33, ” Kwamishinan ya nuna takaicin sa akan hakan musamman ganin ya auku ne tsakanin malamai da daliban su.

Yace ‘yan sanda a jihar ba za suyi kasa-kasa ba wajen hukunta duk wanda aka kama yana aikata irin wannan aiki.

Share.

game da Author

  • Sunana Aliyu ahmad messi daga jihar katsina bakori lga,jargaba,
    akullum ina kara godiya ga allah da zaunar mana da kasa lfy,
    Muna kara mika gaisuwa da barka da zuwa ga baba buhari da yaje asibiti abisa rashin lfy da Allah ya saukar masa Allah yasa kaffarace,

    don Allah kudena zagin baba buhari sabida duk abinda kuga gani to daga Allah ne, Allah shi ya zaba mana shi don ya jagorancemu to saboda haka yan uwa musulmi don Allah adena zagin baba buhari,
    ALLAH KaBa baba buhari lfy,