A karo na biyu, majalisar dattijai ta ki amincewa da nadin Ibrahim Magu a matsayin shugaban hukumar EFCC bayan bayyana da yayi a gabanta yau domin tantanceshi.
Hukumar jami’an tsaro na sirri, wato SSS sun sake rubuta wa majalisar dattijai cewa Ibrahim Magu da take tantancewa a majalisar bashi da amana kuma ba mutum bane da za’a amince masa da shugabanci musamman na hukumar.
Sanata Dino Melaye ne ya fadi hakan a daidai ana tantance Ibrahim Magu a zauren majalisar in da yace anashi ganin bai kamata a cigaban da tantance Magu ba ko don saboda wannan zargi da hukumar SSS din ta sake aikowa majalisar.
Duk da cewa ya amsa tambayoyin da majalisar suka yi masa duka daga karshe sun ki amincewa da nadin nasa a dalilin rahoton hukumar SSS din.
Yanzu dai sai dai a kara turo sunan wani kuma.