Majalisar dattijai zata binciki aiyukkan shugaban hukumar inshoran ta kasa, Usman Yusuf

0

Majalisan dattawa ta kafa kwamitin mutane biyar domin gudanar da bincike akan zargin karya dokar aiki da zargin kashe wasu kudade ba tare da izini ba wanda shugaban hukumar inshorar kiwon lafiya ta kasa NHIS Usman Yusuf ya yi.

Da yake tofa albarkacin bakinsa akan maganar Sanata Kabiru Marafa ya ce kamata ya yi a bincike aiyukkan da shugaban hukumar inshoran ke yi duk da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya na da shi a watan Yulin shekarar da ya gabata.

A bayanin da ya yi yace Yusuf ya kashe wasu kudade ba tare da ya nemi cikakken izini ba daga ministan kiwon lafiya Isaac Adewole.

Ana zargin Yusuf da yin watanda da kudaden da suka kai naira miliyan 960 wanda hakan ya wuce kudaden da doka ta bashi ikon kashewa ba tare da amincewar ministan kiwon lafiya.

Bayan haka sanata Marafa ya zargi Yusuf da daukar ma’aikata ta hanyoyin da bai dace ba sannan ya canza ma wasu ma’aikatan wajen aikin bayan basu cancanci haka ba kumaya kara ma wasu ma’aikatan da ba su dace ba girma a hukumar.

Bayan mahawaran da sanatocin suka yi akan aiyukkan shugaban hukumar mataimakin shugaban majalisan dattawan Ike Ekweremadu ya amince wa kwamitin da aka kafa domin binciki wannan zargi da ta gudanar da hakan sannan ta dawo wa majalisa da sakamakon binciken.

‘yan kwamitin sun hada da: Lanre Tejuso, APC-Ogun shugaban kwamitin kiwon lafiya,Ahmed Lawan APC-Yobe, Bassey Akpan, PDP-Akwa Ibom, Ahmed Ogembe PDP-Kogi, da Kabiru Marafa APC-Zamfara.

A wata bincike da wannan gidan jarida tayi akan wannan badakalar, ta gano cewa Yusuf yana ikirari da cewa babu wanda ya isa ya muzguna masa domin shi dan gatan Buhari ne.

Bayan haka kuma angano cewa a dalilin haka Usman Yusuf baya kula ministan kiwon lafiya sannan baya masa ganin ya isa ya bukaci wani abu game da hukumarsa a wajen ministan.

Share.

game da Author