Majalisar dattijai ta kori Hameed Ali, ta ce sai ya saka unifom zata saurare shi

1

Majalisar dattijai ta ta kori shugaban hukumar Kwastam Hameed Ali da ga zauren majalisar bayan ya bayyana a gabanta domin amsa kiran da tayi masa.

Mataimakin shugaban majalisar Ike Ekweremadu wanda shine ya shugabanci zaman majalisar yau yace majalisar ba za ta saurari Hameed Ali ba saboda rashin saka Unifom da bai yi ba.

Ko da yake Hameed Ali yace babu wata doka da tace dole sai ya sa Unifom kafin ya tafi wajen aiki.

Sanata Bala Ibn Na’allah ya karyata hakan inda ya karanta masa wata sashe a dokar kasa da ya tilasta wa duk wani ma’aikacin hukumar Kwastam din saka Unifom.

Sanata Olamilekan Solomon (APC-Lagos), Barnabas Gemade (APC-Benue) da Barau Jibrin (APC-Kano) duk sun koka da kin bin umarnin majalisar da Hameed Ali yayi na zuwa ba tare da ya saka Unifom ba.

Daga karshe majalisar ta kore shi sannan ta ce ya dawo gabanta ranar Laraba mai zuwa sanye da Unifom.

Share.

game da Author