Majalisar dattijai ta dakatar da Ali Ndume

2

Majalisar dattijai ta dakatar da tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar yau a zamanta.

Majalisar ta dakatar da Ndume ne saboda wai shine ya nemi majalisar da ta binciki badakalar siyan motar da ake zargin shugaban majalisar Bukola Saraki da siya ba tare da takardu na ainihi ba da kuma zargin cewa wai sanata Dino Melaye bai gama karatun jami’a ba.

Kwamitin da ta mika sakamakon bincikenta yau a zauren majalisar ta ce sanata Ndume ya yiwa majalisar karya.

Kwamitin ta ba da shawarar a dakatar da Ali Ndume na shekara daya, in da bayan haka majalisar ta amince da dakatar dashi na wata shida.

Share.

game da Author