Wasu Tsofaffin shugabannin kasa Najeriya sun ce abinda ya faru wajen tantance Ibrahim Magu a majalisa ya nuna cewa a gaskiya Buhari bashi da cikakken iko a gwamnatinsa.
“Kowa na yin yadda ya ga dama ne kawai”
Gidan Jaridar PREMIUM TIMES ta tattauna da wadansu tsofaffin shugabannin kasannan guda biyu kuma suka bukaci kada a baiyana sunayensu inda suka nuna bacin ransu akan yadda majalisa ta ki amincewa nadin Ibrahim Magu shugaban hukumar EFCC.
“Ta yaya za’a ce wai shugaban kasa ya aika da sunan mutum sau biyu kuma ace wai majalisa ta ki amincewa dashi saboda wata zargi da akeyi akansa wanda ba’a tabbatar ba.
“Abun da ya faru ya nuna cewa ba Buhari bane ke ainihin jan ragamar wannan gwamnati.”
Shi kuma tsohon shugaban kasa na biyu da ya tattauna da mu, yace a nashi ganin idan dai ba Buhari bane da kansa yake da hannu a wannan abu da faru a majalisa akan wanda ya zaba toh lallai akwai matsala a kan yadda ake gudanar da mulki a kasannan yanzu.
“Sai dai fa idan akwai hannun shugaban Kasa Muhammadu Buhari akan abin da ya faru da Magu amma idan ba haka toh akwai wadanda suka fi karfin Buhari a gwamnatinsa”.
A dalilin abinda ya faru ina ba Buhari shawara da idan bai dauki mataki akan abubuwan da ke faruwa da wadansu ba a gwamnatinsa da wuri wuri ba to zai ko sha mamaki domin kafin ya ankara komai ya lalace.”
Duk da cewa wannan shine karo na biyu da shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu yake bayyana a majalisar dattijai a wannan karon ma bata haifar da da mai Ido ba.
Magu ya bayyana yau kuma ya amsa duka tambayoyin da ‘yan majalisar suka tambayeshi amma kash, majalisar bata amince da bayanan da ya bada kan rahoton hukumar tsaro na sirri wato SSS in da tace Magu ba mutumin kirki bane da za’a amince da shi.
Cikin dalilan da ya sa majalisar taki amincewa da tabbatar da shi shugaban hukumar EFCC din shine wai an taba kama Magu ta takardun hukumar EFCC a gidansa a wancan lokacin wanda hakan saba ma doka ce.
Da akayi masa wannan tambaya, Magu ya tabbatar da hakan amma yace ko a wancan lokacin da aka tambayeshi bayanai akan tafiya da takardun gida da yayi yace ya kai su gida ne domin ya ci gaba da aiki.
Bayan haka an tuhumeshi da zama a gidan wani jami’in soji da ake tuhuma da laifin cin hanci da rashawa, anan ma Magu ya ce bai taba zama a gidan wannan mutumi ba.
Ya shaida wa majalisar cewa gidan da yake zama aciki gidan gwamnati ne wanda gwamnati ta ke biya masa.
Na uku kuma cikin dalilan shine rashin goyon bayan da bai samu ba daga wajen sanatoci.
Yanzu dai haka ya rage wa mai shiga rijiya, ko shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sunan wani, ko kuma ya bar Ibrahim Magu ya ci gaba da zama a kujeran shugaban cin hukumar na wucin gida har sai an nada wani.