Hukumar jami’an tsaro na sirri, wato SSS sun sake rubuta wa majalisar dattijai cewa Ibrahim Magu da take tantancewa yanzu hakan bashi da amana kuma ba mutum bane da za’a amince masa da shugabancin hukumar.
Sanata Dino Melaye ne ya fadi haka a daidai ana tantance Ibrahim Magu a zauren majalisar in da yace anashi ganin bai kamata a cigaban da tantance Magu ba ko don saboda wannan zargi da hukumar SSS din ta sake aikowa majalisar.