Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta zabi Asibitoci 5 domin taimakawa matafiya a hanyar Abuja zuwa Kaduna

0

Gwamnatin tarayya ta zabi asibitoci 5 da za su kula da marasa lafiya a tsawon lokacin da za’ayi ta amfani da filin jirgin saman Kaduna.

Gwamnati tace tayi hakanne saboda wadanda zasu iya samun hadari a hanyar su samu kulawa cikin gaggawa.

Karamin ministan Kiwon Lafiya Osage Ehanire ne ya sanar da a lokacin da suka zoyarci wasu asibitoci a Kaduna.

Ya ce 3 daga cikin asibitocin suna cikin garin Kaduna ne, 2 kuma na cikin garin Abuja.

Asibitocin sun hada da, Asibitin sojojin Saman Najeriya, Asibitin sojoji na 44, Asibitin St. Geralds, Asibitin Kasa dake Abuja da Asibitin koyarwa na jami’ar Abuja dake Gwagwalada.

Shugaban asibitin sojin saman Najeriya dake Kaduna, Gideon Bako ya tabbatar wa ministan cewa a shirye asibitin take domin tunkaran wannan aiki. Sannan y ace suna da kwararrun ma’aikata a asibitin domin duba duk wani mara lafiya.

Ministan ya kara da cewa ma’aikatarsa za ta gyara cibiyoyin kiwon lafiya da suke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna domin domin bada a gajin gaggawa idan ha rana bukatar hakan.

Ya roki gwamnatin jihar Kaduna da ta gaggauta gyara asibitin Doka da ke hanyar Abuja zuwa Kaduna saboda asibitin na da matukar mahimmanci musamman wajen duba marasa lafiya da suke bin hanyar ko da yaushe.

Ministan ya ce ma’aikatarsa za ta hada hannu da hukumar kula da kare haddura na kasa, hukumar kashe wuta, rundunar ‘yan sanda, hukumar bada da agajin gaggawa, ma’aikatar jiragen sama, ma’aikatan tsaro, gwamnatin jihar Kaduna da gwamnatin jihar Niger domin cimma burin ta.

Share.

game da Author