Sakataren gwamnatin tarayya David Babachir yace ba zai halarci zaman kwamitin majalisar dattijai wanda ta umurceshi da ya bayyana a gabanta domin amsa tambayoyi akan korafin da akeyi kan badakalar kwangilar cire ciyawa a jihar Yobe.
Babachir yace dalilin da ya sa ba zai halarci majalisar ba shine cewa maganar badakalar Kwangilar na gaban kotu saboda haka ba zai amsa kiran majalisar ba.
Ita ma kamfanin Rholavision Ltd wanda iatce ta yi aikin cire ciyawar ta ce shugaban ta ba zai samu daman zuwa majalisar ba saboda baya nan.
Babachir ya karyata sakamakon binciken kwamitin na farko inda yace kwamitin bata gaiyace shi ba domin yayi bayani akan abinda ya faru sannan ta yi masa karya akan laifukkan da suke zargin sa yayi.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi watsi da kiran da kwamitin tayi na ya sauke Babachir daga kujeransa saboda bai gamsu da bayanan majalisar ba akan wadannan laifuffuka da suke zargin Babachir ba.