Wata kungiya mai zaman kanta ‘International Women Peace Group’ ta shirya wani taro mai taken ‘Hana yi wa mata kaciya da kare mutuncin su’ domin su tattauna akan illar da ke tattare da yi wa mata kaciya.
Shugaban kungiyar Kemi Olaokun ta ce sun shirya taron ne domin tunawa da ranar mata sannan kuma su shawarci mata kan yadda za su iya yada soyayya a tsakanin mutane, da tabbatar da ganin an samu zaman lafiya a duniya baki daya.
Ta kuma kara da cewa ya kamata mata su fito su yi magana kan hakkinsu da ake tauyewa duk da cewa baza su iya kamanta kansu da maza ba.
Ogunkolade ta ce kamata ya yi mata su wayar da kan mutane akan illolin yi wa mata kaciya musamman a wuraren taron addini, makarantu, wuraren aiki da dai sauransu.
A wata bincike da hukumar majalisar dinkin duniya ta (UNPFA) ta yi a shekarar 2015 ta gano cewa a kasa Najeriya, jihar Osun ta fi yawan matan da aka yi musu kaciya kuma alkalumma ta nuna cewa sun kai adadin kashi 76.3 bisa 100.
Daga karshe ta ce za su iya shawo kan matsalar yi wa mata kaciya idan suka hada hannu da gwamnati domin dakatar da wannan matsala da ya ki ci yaki cinyewa.