Kotu a jihar Kano ta daure Shahararren mawakin hausan nan Sadiq Zazzabi a kurkuku har sai ranar Juma’a da za ta ci gaba da sauraren karan da hukumar tantance fina-finan ta jihar Kano ta shigar akan mawakin.
Ana tuhumar Sadiq Zazzabi da sakin waka ba tare da ya samu shaidar sakin ta ba daga hukumar tantance fina-finai ta jihar Kano.
Sadiq ya musanta hakan inda yace ana muzguna masa ne saboda kawai yayi wa tsohon gwamnan jihar Rabiu Musa kwankwaso waka.
Da yake tattaunawa da gidan jaridar PREMIUM TIMES kan sammacin da aka kai masa jiya Sadiq yace ya mika wakar tasa ga hukumar tantance fina-finai ta Kano tun 6 ga watan Janairu domin a bashi izinin fitar da wakar amma hakan ya gagara har yanzu.
Yace bayan haka kuma hukumar SSS ta gaiyace shi da ya zo yayi mata bayani akan wakan.
“Bayan amsa gaiyatar SSS, na yi musu bayani akan abin da wakar ta kunsa kafin suka sallameni.
A takardar gaiyatar wanda wannan gidan jarida PREMIUM TIMES HAUSA ta gani ana bukatar Sadiq ya zo kotun hukumar tantance finafinai ne dake gidan Audu Bako a Kano gobe domin ba da bayanai akan dalilin da yasa ya saki wakar ba tare da samun ikon yin hakan ba daga hukumar.
Shugaban hukumar Isma’ila Afakallahu ya sanar ma wannan gidan jarida cewa mawakin ya saba dokar hukumar shine ya sa suke gaiyatarsa domin ya bada bayanai akan abinda yasa yaki jiran hukumar ta amince masa da ya saki wakar kawai yayi awon gabansa.