Kira ga Mata: Ku guje wa saka takalma masu tsini saboda illata kashin baya da yakeyi

0

Wani likita a asibitin Makurdi Martins Adejo ya gargadi mata da su yi taka tsantsan da saka takalman masu tsini domin ya na lahanta kashin bayan mutum.

Likitan yace wadannan takalma na illata kashin baya wanda hakan ya kan lalata wasu sassan dake hade da kashin baya bayan illata kashin shi kansa.

Ya kara da cewa takalma masu tsini na kawo matsala a kwiwwowi da gabobi da tafin kafa, sannan kuma yana raunana jijiyoyin dake tafiyar da jinni a jikin mutum.

“ Idan mace ta nace da sa irin wadannan talkalma za ta samu matsala da jijiyoyin ta da kuma gabobin jikinta idan girma ya zo.

Likita Adejo yace dalilin irin wadannan matsaloli da za’a iya samu zai iya kai ga mutum ya kamu da cutar hawan jinni da ciwon suga.

Share.

game da Author