Kasar Saudiya ta yardan ma kasar Iran ta dawo gudanar da aikin Haji

0

Hukumar kasar Saudi Arabiya ta yardan wa kasar Iran da ta dawo gudanar da aikin haji a kasar daga Hajjin bana.

Kasar Saudiyya ta dakatar da kasar Iran daga aikin Haji tun daga bara saboda matsalolin tsaro.

An sami nasaran shawo kan matsalar da kasashen biyu suka samu ne bayan wata ziyara da jami’an kasar Iran din suka kai kasar Saudiyya domin gyara dangantakar su da ta tabarbare tun shekarar bara.

Share.

game da Author