Ministan ma’adinai, Kayode Fayemi ya ce kamfanin Dangote na sarrafa simintin da kasa Najeriya ke bukata yanzu har ma an fara siyar wa kasashen duniya.
Fayemi ya fadi hakan yayin da ya kai wata ziyarar aiki kamfanin da ke Ibese a jihar Ogun.
Ya kara da cewa gwamnati na kokarin ganin ta shawo matsalolin da ake ta fama dashi a wajen hako ma’adinai a kasa Najeriya.
Fayemi ya ce gwamnati ta ziyarci kamfanin ne domin kara fahimtar da mutane rashin illar kafa irin wadannan kamfanoni musamman cewa da akeyi wai yana da illa ga lafiyar mutane da muhallinsu.
Bayan haka wani jami’I a kamfanin mai suna Joseph Makoju ya yi bayanin cewa kamfanin na daya daga cikin mayan kamfanonin da suke hako ma’adinai a kasa Najeriya sannan tana wadatar da kanta da wutan lantarki musamman idan aka dauke na kasa.
Daga karshe wani babban darekta a kamfanin Amando Martines ya nuna wa ministan yadda kamfanin ke gudanar da ayyukanta ta hanyar zagayawa dashi sannan ya shaida masa cewa kamfanin na sarrafa buhunan simitin da ya kai ton miliyan 6 a shekarar bara amma yanzu ya karu zuwa ton miliyan 12 na seminti.