Kungiyar Hisba a jihar Kano ta sanar da kama ‘yan mata karuwai 79 da maza masu shaye-shaye 39 a wani gidan holewa mai suna Hills and Valleys Recreational Centre dake Awakin Kudu a jihar Kano.
Shugaban Hisba a jihar Abba Sufi yace mata 20 daga cikin wadanda aka kama basu wuce shekara 13 zuwa 14.
Yanzu dai za’a kaisu kotu domin yanke musu tara da kuma hora su.