Gwamnan jihar Filato Simon Lalong ya bada kwana uku domin yin juyayi akan rasuwan kwamishin gidaje da tsare-tsare Simon Galadima.
Simon Galadima ya rasu ne a filin motsa jiki na Rwang-pam da ke garin Jos.
Kwamishinan ya yanke jiki ne a daidai suna gudun motsa jiki da safen jiya.
Likitoci sun tabbatar da mutuwar kwamishina.