Jam’iyyar APC zata shiga tsakanin rikicin majalisar dattijai da Hameed Ali

0

Jam’iyyar APC ta yanke hukuncin shiga tsakanin rikicin majalisar dattijai da shugaban hukumar Kwastam na kasa saboda a samu daidaituwa a tsakanin su.

Kakakin jam’iyyar Bolaji Abdullahi ne ya sanar da hakan a wata takarda da ya saka ma hannu yau a Abuja.

Yace shugaban jam’iyyar John Odigie-Oyegun zai jagoranci shugabannin jam’iyyar zuwa ofishin shugaban majalisar dattijai domin sasanta tsakanin majalisar da Hameed Ali.

Share.

game da Author