Shugaban jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria Ibrahim Garba ya tabbatar wa majalisar dattijai cewa sanata Dino Melaye ya kammala karatun digirinsa a jami’ar.
Garba ya fadi hakan ne a wata zama da wata kwamitin majalisar tayi domin gudanar da bincike akan korafin da akeyi cewa wai sanata Dino bai kamala karatun digirinsa ba a jami’ar.
Majilisar ta bukaci shugaban jami’ar Ahmadu Bello da ya bayyana a gabanta domin sanar mata tabbacin gama karatun sanata Dino a jami’ar.
Shugaban jami’ar Ibrahim Garba ya sanarwa kwamitin cewa Dino wanda ake kira Daniel Jonah Melaye a wancan lokacin ya kammala karatunsa na digiri a jami’ar Ahmadu Bello a shekarar 2000 kuma ya karanta Geography ne.
Bayan haka Dino Melaye ya nuna wa majalisan takardunsa na shiga jami’ar, takardar sakamakon kammala karatun sa.
Duk da haka Matthew Urhoghide APC Edo ya bukaci sanatan da ya nuna wa kwamitin takardun kamala karatunsa na ainihi amma yace bai karbe sub a har yanzu.
Melaye ya kara da cewa ya yi bautar kasarsa ne a kwalejin ‘yan sanda ta jihar Kaduna a shekarar 2000-2001.
A yanzu haka kuma wannan kwamiti na bincike korafin da akeyi wai shugaban majalisar dattijai Saraki ya shigo da mota kirar Range Rover wanda harsashi baya shiga kasa Najeriya ba tare da takardun gaskiya ba.