Kakakin hukumar kwastam Joseph Attach ya ce hukumar ta amince ta dakatar da dokar yi wa motoci rijista da ya zamo abin cecekuce tsakanin hukumar da majalisar dattijai.
Shugaban hukumar kwastam Hammed Ali ya amince da ya dakatar da dokar yi wa motoci rajista bayan ganawan sirrin da sukayi da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki.
Hukumar ta yi hakan ne domin samar da maslaha tsakanin ta da majalisar kan rashin jituwar da ke tsakanin bangarorin biyu.
Hukumar ta ce duk da cewa yin rajista da su hakin kowani dan Najeriya ne kuma ganawarsu zai ba kwamitin majalisar da su damar tattaunawa domin gane amfanin da ke tattare da yi wa motoci rajista da hukumar sannan na da mahimanci da hakan yak e da shi wajen bunkasa tattalin arzikin kasa.