Hukumar Inshorar lafiya ta gano masu morewa shirin na boge

0

Hukumar Inshorar lafiya ta kasa NHIS ta cire wadansu da ke amfana da shirin ta da su ka kai 23,000.

Wadanda aka cire din suna morewa shirin ne ba tare da samun sahihiyar amincewar hukumar ba.

Shugaban hukumar Usman Yusuf yace hukumar ta samu nasaran yin hakan a dalilin hadin gwiwwa da tayi da kamfanoni kamar Galaxy Backbone Plc, Nigeria Communications Satellite Limited and the National Identity Management Commission.

Yusuf yace wannan aiki da sukayi ya kawo musu rashin jituwa tsakanin hukumar da ma’aikatun kiwon lafiya na kasa Najeriya.

“ Duk da cewa ma’aikatun kiwon lafiyar na fada da ni akan hakan, ya zama dole mu aikata hakan saboda a samu inganci da nasara a shirin na hukumar.”

Mataimakin jakadan kasar Britaniya a kasa Najeriya, Harriet Thompson, yace amfani ilimin fasaha musamman wajen daidaita kasidu da samar da bayanai akan aiyukan gwamnati zai sauwaka samarda abubuwan more rayuwa ga mutane.

Da yake bada nasa bayanan, ministan wasanni da ci gaban matasa Solomon Dalung, ya shawarci kwararru a fannin ilimin fasaha da suyi amfani da kwarewarsu wajen kawar da talauci a tsakanin musamman matasan ksa Najeriya.

Share.

game da Author