Hukumar EFCC ta kama buhuhuna sha ke da kudi a filin jirgin saman Kaduna

0

Jami’an hukumar EFCC sun kama wadansu buhuhuna shake da kudi daya kai naira miliya 47 a filin jirgin saman Kaduna.

Darektan Hukumar na shiyar Kaduna Ibrahim Bappa yace an kama kudaden ne a lokacin da ake binciken jakukkunan matafiya.

Buhuhunan suna kunshe ne da kudaden da ya kai naira miliyan 47.

Bappa yace da aka bude buhunan an samu bandir din naira 200 har na miliyan 40 da kuma na naira 50 har na miliyan 7.

Yace daga baya wanda yake da mallakin buhuhunan ya baiyana kansa inda ya kasa bada bayanai akan yadda ya samu wadannan kudade.

Hukumar EFCC din dai tace tana nan tana ci gaba da bincike akan hakan.

kudi

Kudi 3

Share.

game da Author