Ministan yada Labarai, Lai Mohammed ya sanar wa manema labarai a fadar shugaban kasa cewa gwamnati ta kafa wata kwamiti domin sasanta tsakanin ta da majalisar kasa.
Majalisar dattijai da fadar shugaban kasa na takun saka a tsakaninsu musamman a wannan dan kwanakin inda a makon da ya gabata majalisar tayi wa shugaban kasa bore da kin zama domin amincewa da nadin sababbin kwamishinonin zabe da ya aika majalisar.
Lai Mohammed ya ce majalisar zartaswan ta amince da ayi hakan domin a samu daidaituwa a tsakaninsu.
Bayan haka kuma ministoci sun bada bayanai akan ayyukan ma’aikatunsu.