Gwamnati Najeriya ta musanta rahotan kungiyar ‘Amnesty Internation’ kan wai tana muzguna ma wasu mabiya kungiyoyi musamman n ‘yan shi’a a kasar da kuma jibanta ta da tayi da kungiyoyin ‘yan ta’adda a kasar.
Gwamnatin Najeriya ta fadi hakan ne a lokacin da ta ke nuna rashin amincewarta da rahotan kungiyar ‘Amnesty International’ ta shekarar 2015/2016 inda ta zargi jami’an tsaron kasar da laifin karya dokar kare hikin dan Adam musamman na mabiya kungiyoyin Biafara, Boko Haram da ‘yan Shi’a.
Rahotan ta kuma zargi gwamnatin Najeriya da yi wa mutane musamman mabiya akidojin Shi’a da na masu fafutukar kirkiro da kasar Biafara Katanga da ga fadin ra’ayinsu ga gwamnatin.
Sun yi nuni da yadda gwamnati ke ci gaba da rike shugaban kungiyar Shi’a Ibrahim El-Zakzaki ba tare da an gurfanar dashi a kutu ba sannan kuma da saba hukuncin kotu kan a sakeshi tare da matar sa.
A nata martanin da ta maida wa kungiyar Amnesty din gwamnati ta kafe kan bakanta na cewa kungiyoyin Biafara da ‘yan Shi’a ‘yan tsagerane domin suna tada zaune tsaye da kuma aikata ayyuka irin na ‘yan ta’adda.
Gwamantin Najeriya ta ce ayyukkan kungiyar ‘yan Shi’aa na kama da ayukkan Boko Haram na tada zaune tsaye a tsakanin mutane wanda a dalilin hakan ya sa gwamnati ke kokarin ganin ta dakatar da ayyukansu kwata-kwata domin a samu zaman lafiya a kasa baki daya.
Duk da cewa rahotannin kungiyar ‘Amnesty International’ ta bada irin wadannna rahotanni, gwamnatin Najeriya ta na nan a matsayarta na ba za sassauta ma wani dan kungiyoyin da suke tahuma da tada zaune tsayi a kasar ba.
A watan Disembar 2016 gwamnatin Najeriya ta ki amincewa da hukuncin da kotu ta yanke kan a saki El-Zakzaky da uwargidansa tun watan Disembar 2015.