Gwamnatin jihar Kaduna za ta je kotu da Audu Maikori

0

Gwamnan jihar Kaduna Mal. Nasir El-Rufa’I ya ce gwamnati maka shugaban kamfanin Chocolate City, Audu Maikori saboda yada jita-jitan karya da yayi wanda hakan ya kawo zaman dar -dar da tashin hankali a wasu sassan kudancin Kaduna.

El-Rufai ya fadi hakan ne yayin da yake amsa tambayoyi a wani taro da aka yi a jihar Legas mai taken “Technology as a Policy Imperative”.   

Jami’an hukumar SSS sun tasa keyar Audu Maikori zuwa ofishin su domin amsa tambayoyi akan wata labarin karya da ya rubuta a shafinsa ta yanar gizo.

Maikori ya rubuta cewa wai an kashe wadansu daliban makarantar koyan aikin malunta dake garin Kafanchan.

Bayan fadin hakan jami’an tsaro sun gudanar da bincike akai inda suka gano cewa hakan bai faru ba.

Maikori daga baya ya bada hakuri, ya ce direban sa ne ya fada masa hakan kuma shi direban ya ce kisan ya hada da kaninsa.

El-Rufa’I yace Maikori ya yi hanzarin rubuta labarin ne a yanar gizo ba tare da ya tabbatar da gaskiyar abin daya faru ba saboda wata manufa.

Ya kuma ce anyi kokarin nuna masa cewa babu gaskiya a labarinsa domin kwalejin ta dakatar da aiyukkan ta tun a watan Nuwamban kafin abun da yace ya faru da daluban ma.

El-Rufa’ I ya ce bayan an gudanar da bincike akan hakan gwamnati ta maka Maikori a kotu.

Gwamnan ya kara da cewa ba zai bari mutane suna yin abin da suka dama a jihar Kaduna ba kawai domin suna da wata manufa boye a cikinsu.

Ya ce dole ne masu yin amfani da sababbin kafafen yada labarai su shiga taitayinsu akan abubuwan da suke saka wa a shafunansu. Su tabbatar sun binciki sahihancin duk wata labari da zasu rubuta saboda gudun tada zaune tsaye.

Share.

game da Author