Gwamnatin tarayya ta fito da wani shiri domin ilmantar da wayar wa mata masu ciki da masu shayarwa abubuwan da ya kamata su sani domin lafiyarsu da na ‘ya’yansu ta hanyar yin amfani da wayar tafi da gidanka.
Shirin mai suna “mNutrition” shiri ne da za ayi amfani da wayar tarho wajen aikawa da sakonni domin wayar da kan mutane abubuwan da ya shafi kiwon lafiyarsu.
Ministan Kiwon Lafiya Isaac Adewale yace gwamnati tayi hakanne domin ta taimakawa mata da yara kanana sanin irin abincin da suke bukata domin samun lafiya.
Yace wannan shiri zai taimaka wajen ganin an sami isar da bayanan da ya kamata mata su sani akan yadda zasu raini cikinsu da kuma yadda zasu shayar da ‘ya’yansu.
Zai kuma bada bayanai akan irin abincin da zai gina jikin yara kanana har ma da uwayen mata.