Gwamnatin Najeriya ta shawarci ‘yan Najeriya da su dan dakatar da tafiya kasar Amurka har sai an samu daidaituwa kan matsalolin da ake fama dashi na hana shigar baki kasar tun hawan Donald Trump kujeran shugabancin kasar.
Mai ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara kan harkokin kasashen waje Abike Dabiri ce ta sanar da hakan.
Abike Dabiri tace sun samu rahoton taso keyan wasu ‘yan Najeriya masu sahihan takardun shiga kasar amma duk da haka jami’an shige da ficen kasar sun koro su gida Najeriya sannan sun soke takardun shiga kasar Amurkan na su.
Ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su dakatar da tafiya kasar har sai an warware matsalolin shige da fice daga kasar wanda sabuwar gwamnati a kasar ta kafa.