Gwamnan Bauchi ya ziyarci filin da ake hako man fetur a Bauchi

0

Gwamnan Jihar Bauchi Mohammed Abubakar, ya kai ziyaran gani da ido wurin da ake gudanar da tonon man fetur a karamar hukumar Alkaleri dake jihar Bauchi.

Gwamna Abubakar da tawogan sa sun duba wuraren da ake gudanar da wannan aikine a makon da ya gabata.

A Shekaran da ya gabata ne Shugaban kamfanin man fetur na kasa wato NNPC, Maikanti Baru, ya tambatar da cewa an samu man fetur a daya daga cikin rijijoyin da ake hakawa a garin Alkalerin.

Daya ke sanar mana da wannan kokari na Gwamna Abubakar, Ahmadu Bauchi ya ce, Gwamna Abubakar ya ziyarci filin da ake hakon mai sanna ya zazzagaya domin gani ma kansa yadda aiki ke gudana daji.

Bauchi Crude

Bayan haka kuma a makon da ya gabata ne gwamnan ya mika ta’aziyyarsa ga sarkin Bauchi Rilwanu Suleiman Adamu kan rasuwar sakataren masarautar Bauchi din.

Allah Yayi wa sakataren Sarkin Bauchi Alh Maidawa Kafi rasuwa a makon da ya gabata yana da Shekaru sama da Casa’in 90, a duniya.

Bauuchi Crude 3

Share.

game da Author