Majalisar wakilai ta nuna rashin gamsuwarta da yadda ake gudanar da ayyuka a filin jirgin saman Kaduna da ake amfani dashi yanzu a maimakon na Abuja da ake gyarawa.
Wani dan majalisa mai suna Hassan Saleh daga jihar Kano yace filin jirgin saman abin kunya ne a garesu kuma idan ba’ayi hankali toh fa tsautsayi kan iya faruwa a filin jirgin.
Yace babu cikakken tsaro a filin jirgin saman. “ Daga kaje filin jirgin saman zaka jami’an tsaron a rude saboda yawan da akayi musu”.
Dan majalisa Adeyinka Ajayi kuma yace filin jirgin saman bai isa jiragen da tashi da sauka a filin ba yanzu.
Ita kuma Nnnenna Ukeje tace sam babu tsari a filin jirgin saman domin kuwa sai da tayi kusan awa daya bayan ta sauka ana neman jakanta ba’a gani ba.