Gwamnan jihar Kaduna Mal. Nasir El-Rufai ya nada sababbin kwamishinoni da majalisar dokokin jihar ta amince masa da ya nada.
An nada kwamishinonin ne a gidan gwamnati na kashim Ibrahim da ke Kaduna.
Gwamnan jihar Kaduna Mal. Nasir El-Rufai ya mika sunayen sababbin kwamishinoni majalisar jihar domin tantance a makon da ya gabata.
Bayan nadin sabbin kwamishinonin da gwamna El-Rufai ya yi anyi ma wa wadansu kwamishinonin canjin ma’aikatu.
Bayan haka kuma an nada wasu sababbin manyan sakatarori a ma’aikatun jihar inda aka sauya wa wadansu daga cikin wadanda suke kai ma’aikatu.
Wadanda aka nada sun hada da Kabiru Mato a matsayin kwamishinan Ayyukan Gona, Umma Hikima, kwamishinan Shari’a, Hafsat Baba, kwamishinan Harkokin Mata da Ja’afaru Sani a matsayin kwamishinan kananan hukumomi.