Wani dan shekara 55 mai suna Magaji Dansale ya yi ma wata Jaririya ‘yar wata 7 fyade a kauyen Marmachi da ke karamar hukumar Musawa jihar Katsina.
Uwar yarinyar mai suna Zeenatu tace ta auri Magaji Dansale ne bayan ta rabu da uban jaririyarta.
Jaririyar dai agola ce a gidan Magaji Dansale.
Zeenatu ta ce ta sha maganin barci ne inda tayi barci mai nauyi wanda hakan ya bashi ikon yi wa ‘yarta fyade.
“ Lokacin da na tashi daga barci zan bata nono sai naga jini a mafitsaranta, daga nan ne hankalina ya tashi
“Ina gaya wa mijina Dansale abinda ke faruwa sai ya fashe da kuka yana cewa wai yanzu za’a fara cewa shine ya yi
“ Da safe ina wanke kayan yarinya ta sai ya kawo mini wandunansa in wanke masa, anan ne naga jini a jikin wata wandunsa guda daya.
Zeenatu ta kara da cewa bayan wani dan lokaci mijin nata ya kawo mata wasu ganyayyaki wai ta ba yarinyar cewa wai basir ne ke damunta.
“ A lokacin da na kaita asibitin Malumfashi sai likitoci suka sanar mini cewa wai lallai an yi mata fyade ne sannan suka sanar wa ‘yan sanda.
Zeenatu tace ita mijinta Dansale ta ke zargi domin su biyu ne kawai a gidan a lokacin da abin ya faru.