Cutar Sankarau: Gwamnatin Tarayya ta tura jami’an kiwon lafiya da magunguna jihar Sokoto da Zamfara

0

Gwamnatin Najeriya ta aika da jami’an kiwon lafiya da magungunan rigakafi jihohin da cutar sankarau ta bullo.

Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ne ya fadi hakan ranar Alhamis ga manema labarai a Abuja.

Yace gwamnati tayi hakanne domin ganin an shawo kan cutar kafin ta yadu wadansu garuruwan.

Bincike ya nuna cewa cutar ta yi ajalin mutane 5 a asibitocin dake garuruwan Gada da Wauru na karamar hukumar Gada a jihar Sokoto sannan kuma an sake samun irin hakan a jihar Zamfara ranar Talatar da ta gabata.

Bayan haka a kowace shekara musamman lokacin rani akan na samun barkewan cutar sankarau da kuma wasu cuttutuka da ta ke kawowa.

A dalilin hakan ne ya sa ma’aikatar kiwon lafiya ke iya kokarin ta domin gannin cewa ta kawar da cuttutukan a yakin arewacin kasan musamman a jihar Sokoto da Zamfara ta hanyar tattaunawa da kwamishanonin kiwon lafiyan jihohin, wadatar da magungunan rigakafi da ma’aikatan da asibitocin yankin za su bukata.

Daga karshe ya shawarci mutanen musamman na yakin arewacin kasar da su kai duk wanda ya kamu da cutar zazzabi ta kowace iri ko kuma tari zuwa asibiti.

Ya kuma ce a rage yawan cinkoso a wuri daya sannan a yawaita bude tagogi domin samun isashshen iska wanda hakan zai rage yawan kamuwa da cutar.

Share.

game da Author