A shekarar 2009, uwargidan tsohon shugaban kasa Turai ‘yarAdu’a ta kaddamar da wata cibiya domin kula da masu dauke da cutar daji, wato Cancer.
Tun bayan wannan buki da akayi na kaddamar da sabon cibiyar komai ya tsaya cak.
Duk da cewa cibiyar ta samu makudan kudi daga attajiran kasa Najeriya da kungiyoyin bada agaji dabam dabam na duniya bata fara aiki ba tun bayan hakan.
A wata bincike da gidan jaridar PREMIUM TIMES ta yi akan halin da cibiyar ta ke ciki ya nuna yadda ginin ofishin ya zama kusan kango.
Bayanai ya nuna cewa akwai wasu lokutta a baya da barayi suka sace kayayyakin wutan ofishin da ya hada da wayoyi da dai wasu abubuwan da ba’a sani ba.
Makasudin gina wannan cibiya dama saboda a wadata ta da kayayyakin duba masu fama da cutar daji ne da kuma taimakawa talakawa musamman wadanda suke fama cutar su sami magani cikin sauki.
Ginin dai nan nan a tsaye a babban birnin tarayya, Abuja zagaye da ciyayi a ko ina a cikin ginin. Sannan kuma ga motoci da suka kai kusan 200 a jiye cikin kura. Wasu ma sun fara fita daga haiyacinsu.