Buhari ya mika sunayen Ministoci biyu Majalisar Dattijai domin tantancesu

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aika da sunaye biyu domin tantacesu a majalisar dattijai don zama ministoci a kasa Najieriya.

Wadanda aka aika da sunayensu sun hada da Stephen Ocheni daga jihar kogi wanda zai cika gurbin kujeran minista daga jihar ne wanda tun bayan rasuwar tsohon ministan James Ocholi ba’a nada wani ba,shi kuma Suleiman Hassan daga jihar Gombe zai canji amina Zubbair da ta koma aiki majalisar dinkin duniya.

Shugaban Majilisar dattijai Bukola Saraki ne ya karanta wasikar a zauren majalisar yau Laraba.

Har yanzu dai ana zaman doya da manja ne tsakanin majalisar da fadar shugaban kasa in da majalisar ta ki zama jiya domin tantance kwamishinonin zabe da shugaban kasa ya aika majalisar saboda kin tsige shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu da Buhari bai yi ba.

Share.

game da Author