Tsohon shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar wakilai Abdulmumini Jibrin yace shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai iya cigaba da rike kasa Najeriya ba saboda haka ya sauka daga kujeran shugabancin kasa Najeriya.
Abdulmumini Jibrin ya na wakiltan kiru/Bebeji, dake jihar Kano.
Abdulmumini Jibrin yace rashin lafiyar Buhari ya hana shi yin komai a kasa Najeriya.
” Najeriya ta wuce ace wai shugaban kasar ta na maneji ne kamar dole.
” Shugaban kasan da nike gani a talabijin shugabane da yake bukatar Hutu, Kula, da samun isasshen lokaci da iyalansa.
” Rayuwa da mutuwa duk na Allah ne amma shugaban kasa na matukar neman hutu yanzu.
Saboda haka yayi kira ga Buhari da ya hakura da mulki ya ajiye hakanan.