Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta sha kayi a hannun Deportivo da ci 2 da 1.
Rashin shahararren dan wasanta Neymar ya nuna karara inda Messi ya kasa nuna bajinta wajen taimakawa Barcelona cin wasan.
Real Madrid kuma ta lallasa Betis da ci 2 da 1 inda yasa ta dare saman laliga duk da ta na da kwanton wasa daya.
Yau ne za’a kara tsakanin kungiyar kwallon kafa na Chelsea da na Manchester United a wasan cin kofin FA.