Bankuna uku na shirin kwace kamfanin sadarwa ta ETISALAT

2

Bankunan Guarantee Trust, Zenith da Access na shirin kwace kamfanin sadarwa ta Etisalat saboda bashin biliyoyin naira da take bin Kamfanin.

Bankunan na bin kamfanin Etisalat bashin sama da naira biliyan N540.

Kamfanin Etisalata na da masu amfani da layinta sama da mutane miliyan 21 a wata kididdiga da akayi a watan Janairun 2017.

Kamfanin ta koka da tabarbarewan tattalin arzikin kasa a matsayin dalilan da ya sa kamfanin ta gagara biyan basussukan.

Wani babban darekta a hukumar NCC yace hukumar ta yardan ma bankunan da su kwace kamfanin a matsayin bashinsu.

Share.

game da Author