Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya ce bashi bane ya fitar da wasikar da ya rubuta wa Buhari.
El-Rufai ya fadi hakanne a wata hira da yayi da taridar Daily Trust na ranar Lahadi.
A hirar yace wasikar sa yayi ta ne tsakaninsa da Buhari bai taba tunanin ya bari duniya ta sani ba, kuma da ya so hakan da tuntuni ya fitar amma bai yi ba.
El-Rufai yace wasu ne kawai da suke adawa da shi saboda matukar soyayya da yake nuna wa Buhari ke yi masa zagon kasa.
“Ba ni bane na fitar da wasikar ba kuma idan har nine babu abinda zai hana ni fadin haka, amma ina son kowa ya sani yau cewa bani bane na fitar da wasikar da na rubuta wa Buhari kuma har yanzu ina kokarin gano dalilin da yasa wadanda suka fitar sukayi hakan ganin cewa wasikar ba na yi ta bane domin idanun duniya, tsakanina ne da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
“Ina ganin na rubuta wa Buhari wasiku da suka kai sama da goma tun daga lokacin da na sanshi zuwa yanzu kuma dukkansu sai naga wani abu da yake neman a gyara wanda shi bai ankare ba sai in rubuta domin sanar masa.
“Na rubuta wannan wasika ne domin ganin cewa abubuwa da yawa basa tafiya yadda ya kamata kuma mune muka kusa da talakawa muna jin irin kukansu.
“Ina daya daga cikin mutane 34 da suka saka hannau a hukumar zabe domin rijistan jam’iyyar APC. Ina daga cikin wadanda suka rubuta kundin tsarin gudanar da mulki jam’iyyar APC saboda haka ina ganin jam’iyyar APC daya daga cikin ‘ya’ya na ne nima.
“Amma daga baya sai muka ga cewa wasu dabam sun karkata akalan zuwa wata hanyar da bashi bane manufar kafa Jam’iyyar da kuma abinda shi kansa Buhari yake shirin yi.
“Na kwashe tsawon shekaru bakwai ina karantar wanene Buhari sannan ina yi masa aiki duk domin a samu nasarar gyara kasa Najeriya.
“Na yi matukar yarda da Buhari, kuma ni masoyinsa ne na kwarai.
“Buhari kamar uba ne a wurine kuma ya zama dole in yi duk abinda zan yi domin ganin na sanar dashi abinda ke guda a kasa-kasa da bai sani ba.
“El- Rufai yace shine fa ya rubuta wannan wasika idan da yaso ya fitar tun a wancan lokacin da yayi hakan amma tana ajiye a wurinsa.
“Duk wanda ya karanta wasikar zai san cewa babu wata abin tashin hankali akai.
“Babu wani wuri a cikin wasikara da nace wai gwamnatin Buhari ta gaza.
“Gwamnatin mu ne idan ta gaza toh muma zai shafe mu dole domin zai nuna mun gaza kenan.
“Amma yanzu siyasa akeyi kuma na tsole wa mutane da yawa ido wanda bansan dalili ba. Kuma duk abubuwan da ke cikin wasikar shawarwari ne da tunatarwa amma babu wani abu da ya wuce haka.
“Ina tare da shugaban kasa tun 2010 kuma a duk lokacin da na rubuta masa wasika kuma ya tattauna da na kusa dashi sai suce masa wai ni ina da wata boyayyiyar manufa ko kwadayin mulki.
“An sha cewa wai ina so in zama shugaban kasa a Najeriya tun 2007 kuma a dalilin hakan ya sa dole na gudu na bar kasa Najeriya a lokacin mulkin Umaru Musa Yar’adua.”