Kotu a jihar Adamawa ta yanke wa tsohon gwamnan jihar Adamawa din James Bala Ingilari, daurin shekara biyar a gidan yari saboda kamashi da tayi da hannu dumu-dumu wajen sabawa ka’idojin da doka ta bayar kan yadda za’a bada kwangiloli a jihar.
An daure tsohon gwamna Ingiari har na tsawon shekara biyar a kurkuku.
A hukuncin da alkalin kotun ya yanke Nathalian Musa, yace an kama Ingilari da aikata laifuffuka hudu cikin biyar din da ake tuhumarsa akai a karar.
Da yake bayani akan rashin ba Ingilari damar biyan Tara ba, yace yayi hakanne saboda doka bata ba da wannan damar ba.
Da ga karshe Alkali Musa y ace tsohon gwamna Ingilari ya zabi duk kurkukun da yake so yayi zaman wakafin a ciki.
Ko da yake tsohon gwamnan ya nuna rashin amincewarsa da hukuncin kotun ya shaida wa manema labarai bayan zaman kotun cewa tabbas zai kalubalanci wannan hukunci a kotun koli.