Bamu gamsu da aikin da akeyi a filin jirgin saman Abuja ba

0

Kwamitin majalisar wakilai ta ce ba ta gamsu da aikin da akeyi a filin jirgin saman Abuja ba.

Shugaban kwamitin harkokin jiragen sama na majalisar Nkiruka ta ce abinda kwamitin ta gani bai gamsar dasu ba ko kadan.

Ta ce a yadda taga ana aikin filin jirgin ba ta ga alamar cewa wai za’a gama aikin nan da makonni 3 da suka rage ba.

Ministan sufurin jiragen saman Hadi Sirika ya ce yana da yakinin cewa za’a gama aikin kamar yadda ‘yan kwangilan suka yi alkawari.

Sannan kuma ya karyata rade-radin da ake ta yadawa wai gwamnati ta kara tsawon kwanakin aikin zuwa makonni 18 nan gaba.

Share.

game da Author