Bamabamai sun tashi a garin Maiduguri da safen yau.
Bam din sun tashi ne a titin Damboa dake kusa da ma’ajiyar man na kamfanin matatan mai (NNPC).
Wani mazaunin Unguwan Damboa Abubakar Kaumi yace wata mata ce da wadansu yan mata biyu dauke da bamabamai suka tada bama din kusa da wadansu tankoki dauke da mai.