Kakakin Majalisar wakilai Yakubu Dogara y ace bai ga dalilin da ya sa Majalaisar dattijai ke sa’insa da shugaban hukumar Kaeastam, Hameed Ali ba.
Yakubu Dogara yace a nasa ganin hakan duk dagula aiki ne amma ba abinda ya kamata ce wai ya ana tra cece-kuce akai bane.
Dogara ya fadi hakanne da yake ganawa da editocin gidajen jaridu a majalisar wakilai din.
Yace kamata yayi majalisar ta mai da hankalinta akan nasarorin da ake samu a hukumar da yadda ta ke gudanar da aiyukanta mai makon abin da ake ta cece-kuce akai.
Kakakin yace duk da cewa akwai maganar duba dalilan da ya jawo sa-insan da majalisar dattawa da shugaban hukumar kwastam din suke yi a gaban majalisar wakilai, ba zai iya cewa komai akai ba yanzu sai sun zauna a zauren majalisa da sauran wakilai.