Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace Najeriya ba za ta sake yarda tayi sakaci wasu ‘yan ta’adda su kwace wani yanki na kasar nan ba.
Buhari ya fadi hakanne a dajin Sambisa wajen bude bikin wasannin soji na farko da za’ayi a dajin.
Ministan tsaro Mansur Dan-Ali ne ya wakilci shugaban kasan a wajen bude bikin wasannin sojin.
Janar David Ahmadau wanda shine shugaban shirya wasan yace an shirya wannan gasar ne a dajin Sambisa saboda a nuna wa mutane cewa an fa kwato dajin daga hannun kungiyar Boko Haram sannan sojin Najeriya din ta mai da dajin filin gudanar da gasar ayyukan soji na kasa daga yanzu.
Yace za’a kara ne tsakanin sansanonin sojoji dabam da bam inda sansanin da tayi fice za a bata kofi, mai suna kofin babban hafsan sojin Najeriya.