Arsenal ta dandana kudanta a hannun Bayern Munich da ci 10 da 2

0

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta sha kashi a hannun Bayern Munich da ci 10 da biyu a wasan zakarun kwallon kafa na nahiyar turai.

Bayern ta lallasa Arsenal a karawarsu na farko a kasar Jamus da ci 5 da 1 inda suka kara doke su da ci 5 da 1 a bugawa ta biyu yau.

Bayern ne ta samu wucewa rukunin kifa daya kwala wanda za’a fara bugawa bayan sauran kungiyoyin sun buga nasu wasannin.

A wasa ta biyu kuma Real Madrid ta doke Napoli na kasar Italiya da ci 3 da 1.

Gobe ne kungiyar kwallon kafa ta Barcelona zata buga da takwaranta PSG a filin Nuo Camp.

Share.

game da Author