An soke rakumi domin murnan dawowar Buhari a garin Bauchi

0

Ranar Asabar din nan ne dubban masoya shugaban Kasa Muhammadu Buhari a jihar Bauchi suka fito domin ci gaba da nuna farin cikinsu da dawowar shugaban kasa daga kasar Ingila.

Shugaban matasan jam’iyyar APC na jihar Bauchi Alh. Nasiru Umar Gwallaga kuma sarkin yakin bakan Kasar Kobi ne ya jagoranci wannan gangami.

Mata da maza, yara da manya duk sun amsa kiran Gwallaga sun fito titunan garin Bauchi domin bada nasu gudunmawar ga wannan taro.

Gwallaga ya kuma soke rakumi sannan ya bada sadakar naman ga mutane domin ci gaba da yi wa Buhari addu’ar samun lafiya mai dorewa.

Shuagabn Kasa Muhammadu Buhari ya dawo kasa Najeriya ranar Juma’a daga kasa Najeriya bayan ya shafe kwanaki 51 a kasar ingila yana ganin likitocinsa.

Rakumi 2

Rakumi 1

Share.

game da Author