Kwamishinan ilimin jihar Bauchi wanda shine mataimakin gwamnan jihar ya bada Umurnin rufe Makaranta Sa’adu Zungur saboda zargin rashin tarbiyya da yaran makarantar suke yi.
Mataimakin Gwamnan jihar Bauchi, wanda shine yake rike da mukamin kwamishinan ilimi na jihar, a wata ziyarar bazata da ya kai makarantar Sa’adu Zungur Model Primary and Secondary School dake garin Bauchi, ya bada umarnin rufe makarantar na wucin gadi har zuwa ranar laraba mai zuwa wato, 15 ga watan Maris, 2017 sakamakon abunda ya faru na rashin tarbiya a makarantar.
An samu rahoton aukuwar auren wasa tsakanin wasu daliban makarantar guda biyu.
Kwamishinan Ilimin ya dauki wannan mataki ne a ranar juma’a 10th, March, 2017 bayan yayi fatali da rahoton kwamitin binciken da ya kafa a farko.
Nuhu Gidado ya umarci daukacin Daraktocin dake Ma’aikatar, hukumar makarantar, malamai, da Kungiyar Iyaye da malamai wato (PTA) da su hadu domin bincikar wannan al’amari tare da gabatar da sahihin rahoto kafin a sake bude makarantar a ranar laraba, ba tare an kyale wani mai laifi ba ko an ware wasu ba.
Daga karshe Nuhu Gidado ya jaddada aniyar gwamnatin jihar Bauchi na magance sakaci da’ake yi a makarantun gwamnati tare da tabbatar da kawo karshen irin wadannan ayyuka na rashin tarbiyya a tsakanin dalibai a makarantun.
An ce wani dalibi ya biya naira 500 a matsayin sadakin wata daliba wai don suyi aure. Bayan haka abokanan su ‘yan ajin suka tara kudi suka siya lemo da kayan ciyeciye domin bukin auren da sukayi a jin makarantar.
Hakan dai shini daya daga cikin irin wannnan aure da kayi ta yi a makarantar.